4 Gari na wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba.
5 Sai Yesu ya ce musu, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “A'a.”
6 Ya ce musu, “Ku jefa taru dama da jirgin za ku samu.” Suka jefa, har suka kāsa jawo shi don yawan kifin.
7 Sai almajirin nan da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ubangiji ne dai!” Da Bitrus ya ji, ashe, Ubangiji ne ya yi ɗamara da taguwarsa, don a tuɓe yake, ya fāɗa tekun.
8 Sauran almajirai kuwa suka zo a cikin ƙaramin jirgi, janye da tarun cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, kamar misalin kamu ɗari biyu ne.
9 Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi kai, da kuma gurasa.
10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi a na waɗanda kuka kama yanzu.”