9 Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi kai, da kuma gurasa.
10 Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi a na waɗanda kuka kama yanzu.”
11 Sai Bitrus ya hau jirgin, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu haka, tarun bai kece ba.
12 Sai Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Daga cikin almajiran kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin tambayarsa ko shi wane ne, domin sun sani Ubangiji ne.
13 Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin.
14 Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.
15 Da suka karya kumallo Yesu ya ce wa Bitrus, “Bitrus ɗan Yahaya, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon 'ya'yan tumakina.”