19 Matar ta ce masa, “Ya Shugaba, na dai gane kai annabi ne.
20 Kakanninmu sun yi sujada a dutsen nan. Ku kuwa kun ce a Urushalima ne wurin da ya wajaba a yi sujada yake.”
21 Sai Yesu ya ce mata, “Uwargida, ki gaskata ni, lokaci na zuwa da ba za ku yi wa Uba sujada ba, ko a kan dutsen nan, ko a Urushalima,
22 Ku kuna yi wa abin da ba ku sani ba sujada, mu kuwa muna yi wa abin da muka sani sujada, domin ceto ta hanyar Yahudawa yake.
23 Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a ruhu, da gaskiya kuma. Lalle kuwa irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.
24 Allah Ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa lalle su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”
25 Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.”