40 Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan.
41 Waɗansu kumma da yawa fiye da na dā suka ba da gaskiya saboda magana tasa.
42 Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”
43 Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili.
44 Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu.
45 Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin.
46 Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani bafada wanda ɗansa ba shi da lafiya.