44 Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu.
45 Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin.
46 Sai ya sāke zuwa Kana ta ƙasar Galili, inda ya mai da ruwa ruwan inabi. A Kafarnahum kuwa akwai wani bafada wanda ɗansa ba shi da lafiya.
47 Da jin cewa Yesu ya fito ƙasar Yahudiya ya komo ƙasar Galili, sai ya tafi wurinsa, ya roƙe shi ya je ya warkar da ɗansa, don yana bakin mutuwa.
48 Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”
49 Sai bafadan nan ya ce masa, “Ya Shugaba, ka zo tun ƙaramin ɗana bai mutu ba.”
50 Yesu ya ce masa, “Yi tafiyarka, ɗanka a raye yake.” Mutumin kuwa ya gaskata maganar da Yesu ya faɗa masa, ya yi tafiyarsa.