7 Marar lafiyar ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, ai, ba ni da wanda zai angaza ni cikin ruwan lokacin da aka motsa shi. Lokacin da na doshi ruwan kuma sai wani ya riga ni shiga.”
8 Sai Yesu ya ce masa, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka, ka yi tafiya!”
9 Nan take mutumin ya warke, ya ɗauki shimfiɗarsa ya yi tafiya tasa.Ran nan kuwa Asabar ce.
10 Saboda haka Yahudawa suka ce da wanda aka warkar ɗin, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka ɗauki shimfiɗarka ba.”
11 Sai ya amsa musu ya ce, “Ai, wanda ya warkar da ni, shi ne ya ce in ɗauki shimfiɗata, in tafi.”
12 Suka tambaye shi, “Wane mutum ne ya ce maka ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi?”
13 Wanda aka warkar ɗin kuwa bai san ko wane ne ba, domin Yesu ya riga ya tashi saboda taron da yake wurin.