12 Da suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka saura, kada kome ya ɓata.”
13 Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha'ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu.
14 Da jama'a suka ga mu'ujizar da ya yi, suka ce, “Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya.!”
15 Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.
16 Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.
17 Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna.
18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa.