16 Da magariba ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.
17 Suka shiga jirgi suka tasar wa haye tekun zuwa Kafarnahun. A sa'an nan duhu ya yi, Yesu kuwa bai zo wurinsu ba tukuna.
18 Sai tekun ta fara hauka saboda wata riƙaƙƙiyar iska da take busowa.
19 Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita.
20 Amma ya ce musu, “Ni ne, kada ku ji tsoro.”
21 Sa'an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.
22 Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai wani ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi.