1 Bayan haka, Yesu ya riƙa zagawa a Ƙasar Galili, bai yarda ya zaga ta Yahudiya ba, don Yahudawa suna neman kashe shi.
2 Idin Bukkoki na Yahudawa kuwa ya gabato.
3 Sai 'yan'uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi.
4 Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al'amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.”