27 Wannan kam, mun san daga inda yake, amma sa'ad da Almasihu ya zo ba wanda zai san daga inda yake.”
28 Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba.
29 Ni na san shi, domin daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.”
30 Don haka suka nema su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.
31 Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa'ad da Almasihu ya zo, zai yi mu'ujizai fiye da na mutumin nan?”
32 Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi.
33 Sai Yesu ya ce, “Saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku, sa'an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni.