2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Ya Shugaba, wa ya yi zunubi da aka haifi mutumin nan makaho, shi, ko iyayensa?”
3 Yesu ya amsa ya ce, “Ba domin mutumin nan ko iyayensa sun yi zunubi ba, sai domin a nuna aikin Allah ne a kansa.
4 Lalle ne mu yi aikin wanda ya aiko ni tun da sauran rana. Ai, dare zai yi sa'ad da ba mai iya aiki.
5 Muddin ina duniya ni ne hasken duniya.”
6 Da ya faɗi haka sai ya tofa yau a ƙasa, ya cuɗa ƙasa, ya shafa a idanun makahon,
7 ya ce masa, “Je ka, ka wanke ido a ruwan Siluwam,” wato aikakke. Shi ke nan sai ya je ya wanke ido, ya komo yana gani.
8 Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”