1 Ya ku 'yan'uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.
2 Misali, in mutum mai zobban zinariya da tufafi masu ƙawa ya halarci taronku, wani matalauci kuma ya shigo a saye da tsummoki,
3 sa'an nan kuka kula da mai tufafi masu ƙawar nan, har kuka ce masa, “Ga mazauni mai kyau a nan,” matalaucin nan kuwa kuka ce masa, “Tsaya daga can,” ko kuwa, “Zauna a nan ƙasa a gabana,”
4 ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani?
5 Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba?
7 Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba?