4 ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani?
5 Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
6 Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba?
7 Ba kuma su ne kuke saɓon sunan nan mai girma da ake kiranku da shi ba?
8 Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.
9 Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni.
10 Duk wanda yake kiyaye dukkan Shari'a, amma ya saɓa a kan abu guda, ya saɓi Shari'a gaba ɗaya ke nan.