1 Sa'an nan Sama'ila ya ɗauki 'yar kwalabar mai, ya zuba wa Saul a kā, ya yi masa sumba, ya ce, “Ubangjiji ne ya keɓe ka, ya naɗa ka sarki a kan jama'arsa.
2 Yau, sa'ad da ka rabu da ni, za ka gamu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a karkarar Biliyaminu a Zelza. Za su ce maka, jakunan da ka tafi nema an same su, yanzu mahaifinka ya daina damuwa saboda jakunan, sai a kanku, yana cewa, ‘Ina zan gane ɗana?’
3 Sa'ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da 'yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.
4 Za su gaishe ka, su ba ka malmala biyu, kai kuwa sai ka karɓa.
5 Sa'ad da ka isa Gibeya, wato tudun Allah, inda sansanin sojojin Filistiyawa yake, a nan kuma sa'ad da kake shiga garin, za ka tarar da ƙungiyar annabawa suna gangarowa daga wurin bagaden a kan tudu suna kaɗa garaya, da kuwaru, da sarewa, da molo, suna rawa suna sowa.
6 Sa'an nan Ruhun Ubangiji zai sauko maka, za ka kuwa yi rawa da sowa tare da su, za ka zama wani mutum dabam.
7 Sa'ad da waɗannan alamu suka cika, sai ka yi abin da hali ya nuna maka, gama Ubangiji yana tare da kai.