1 Sam 15 HAU

Yaƙi da Amalekawa

1 Sama'ila ya ce wa Saul, “Ubangiji ya aike ni in zuba maka man keɓewa don ka zama sarkin mutanensa, Isra'ila. Yanzu sai ka yi biyayya da maganar Ubangiji.

2 Zai hukunta Amalekawa saboda sun yi gāba da Isra'ilawa lokacin da suke tahowa daga Masar.

3 Ka tafi yanzu, ka fāɗa wa Amalekawa da yaƙi. Ka hallakar da dukan abin da suke da shi. Kada ka rage kome, ka karkashe su dukka, da mata da maza, da yara da jarirai, da takarkarai, da tumaki, da raƙuma, da jakai.”

4 Saul kuwa ya kira mutanen da ya ƙidaya a Telem, sojoji dubu ɗari biyu (200,000) daga Isra'ila, da dubu goma (10,000) daga Yahuza.

5 Sa'an nan Saul ya zo birnin Amalekawa ya yi kwanto a cikin kwari.

6 Ya ce wa Keniyawa, “Ku tafi, ku rabu da Amalekawa, don kada in hallaka ku tare da su, gama kun yi wa dukan Isra'ilawa karamci lokacin da suka fito daga Masar.” Keniyawa kuwa suka fita daga cikin Amalekawa.

7 Saul ya ci Amalekawa, tun daga Hawila har zuwa Shur, da yake gabashin Masar,

8 ya kama Agag Sarkin Amalekawa da rai, ya hallaka mutane ƙaƙaf da takobi.

9 Amma Saul da jama'arsa suka bar Agag da rai, ba su kuma kashe tumaki da takarkarai mafi kyau ba, da 'yan maruƙa, da raguna, da dukan abin da yake mai kyau, bai yarda su hallaka su duka ba, amma sun hallaka dukan abin da yake rainanne ko marar amfani.

An Ƙi Saul da Zaman Sarauta

10-11 Sai Ubangiji ya yi magana da Sama'ila ya ce, “Na yi baƙin ciki da na sa Saul ya zama sarki, gama ya rabu da ni, ya yi rashin biyayya ga umarnaina,” Sama'ila kuwa ya yi fushi, ya yi ta roƙo ga Ubangiji dukan dare.

12 Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal.

13 Sai Sama'ila ya tafi wurin Saul, Saul kuwa ya gaishe shi, ya ce, “Ubangiji ya sa maka albarka, Sama'ila, na yi biyayya ga umarninsa.”

14 Sama'ila ya ce masa, “To, ina baicin wannan kukan shanu da na tumaki da nake ji?”

15 Saul kuwa ya ce, “Ai, mutanena ne suka kawo su daga Amalekawa. Gama sun bar mafi kyau na tumaki, da na shanu domin su miƙa su sadaka ga Ubangiji Allahnka. Mun hallaka sauran ƙaƙaf.”

16 Sa'an nan Sama'ila ya ce wa Saul, “Dakata, in faɗa maka abin da Ubangiji ya faɗa mini a daren jiya.” Sai Saul ya ce, “Faɗa mini.”

17 Sama'ila ya ce, “Ko da yake kana ganin kanka kai ba wani abu ne ba, ashe, ba kai ne yanzu shugaban kabilan Isra'ila ba? Ubangiji ya sa ka zama Sarkin Isra'ila,

18 ya kuma umarce ka ka tafi ka hallakar da waɗannan mugayen mutane, wato Amalekawa. Ya faɗa maka ka yi yaƙi, har ka hallaka su ƙaƙaf, kada ka rage ko guda ɗaya.

19 Me ya sa ba ka yi biyayya da shi ba? Don me ka fāɗa wason ganima, ka yi abin da Ubangiji ba ya so?”

20 Sai Saul ya amsa wa Sama'ila, ya ce, “Na yi wa Ubangiji biyayya, gama na tafi kamar yadda ya faɗa mini, na kamo sarki Agag, na kuma hallaka Amalekawa ƙaƙaf.

21 Amma mutanena ba su kashe tumaki da shanu mafi kyau ba, amma suka kawo su domin sadaka ga Ubangiji Allahnka a Gilgal.”

22 Sai Sama'ila ya ce, “Me Ubangiji ya fi so? Biyayya, ko kuwa sadakoki da hadayu? Ya fi kyau a yi masa biyayya, da a miƙa masa hadayar tumaki mafi kyau.

23 Gama tayarwa kamar zunubin bokanci take. Taurinkai kuma kamar bautar gumaka yake. Kamar yadda ka ƙi umarnin Ubangiji, haka nan shi ma ya ƙi ka da zama sarki.”

24 Sa'an nan Saul ya ce wa Sama'ila, “Na yi zunubi, na yi rashin biyayya ga umarnin Ubangiji da kuma koyarwarsa. Na ji tsoron mutanena, na kuwa biye wa abin da suke so.

25 Yanzu fa, ina roƙonka ka gafarta mini zunubina, ka koma tare da ni domin in yi wa Ubangiji sujada.”

26 Sama'ila ya ce wa Saul, “Ba zan tafi tare da kai ba, gama ka ƙi umarnin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ƙi ka da zama Sarkin Isra'ila.”

27 Sa'an nan Sama'ila ya juya zai tafi, amma Saul ya kama alkyabbar Sama'ila, sai ta yage.

28 Sai Sama'ila ya ce masa, “Yau Ubangiji ya yage sarautar Isra'ila daga gare ka. Ya ba da ita ga maƙwabcinka wanda ya fi ka.

29 Gama Maɗaukaki na Isra'ila ba zai yi ƙarya, ko ya sāke nufinsa ba. Shi ba mutum ba ne, da zai sāke nufinsa.”

30 Sai Saul ya ce, “Na yi zunubi, amma duk da haka ka darajanta ni a gaban shugabannin mutanena, da gaban Isra'ilawa, ka zo, mu tafi tare domin in yi wa Ubangiji Allah sujada.”

31 Sama'ila kuwa ya tafi tare da Saul, Saul kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.

32 Sa'an nan Sama'ila ya ce, “Ku kawo mini Agag Sarkin Amalekawa.” Sai Agag ya taho wurinsa, yana rawar jiki don tsoro, yana cewa a ransa, “Hakika, azabar mutuwa ta fi ɗaci.”

33 Sama'ila ya ce masa, “Kamar yadda takobinka ya mai da mata marasa 'ya'ya, haka za a mai da mahaifiyarka ta zama marar ɗa.” Sai Sama'ila ya sassare Agag gunduwa gunduwa a gaban bagade a Gilgal.

34 Sa'an nan Sama'ila ya tafi Rama, Saul kuwa ya tafi gidansa a Gibeya.

35 Daga ran nan Sama'ila bai ƙara saduwa da sarki Saul ba, har rasuwar Sama'ila, amma ya ji juyayin Saul. Ubangiji kuwa bai ji daɗi da ya sa Saul ya zama Sarkin Isra'ila ba.

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31