18 Dawuda, ya ce wa Saul, “Wane ni ko iyalin mahaifina a cikin Isra'ila, har da zan zama surukin sarki?”
19 Amma sa'ad da lokaci ya yi da za a ba Dawuda Merab, 'yar Saul, ya aura, sai aka aurar da ita ga Adriyel, mutumin Abel-mehola.
20 Mikal, 'yar Saul kuwa, ta ƙaunaci Dawuda, sai aka faɗa wa Saul, shi kuwa ya yarda da haka.
21 Ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan ba shi ita don ta zamar masa sanadin da zai mutu ta hannun Filistiyawa.” Don haka sai Saul ya ce wa Dawuda a karo na biyu, “Yanzu dai za ka zama surukina.”
22 Sai Saul ya umarci fādawansa, ya ce, “Ku yi magana da Dawuda a ɓoye, ku ce masa, ‘Ga shi, sarki yana jin daɗinka, dukan fādawansa kuma suna ƙaunarka, yanzu sai ka zama surukin sarki.’ ”
23 Fādawan Saul kuwa suka faɗa wa Dawuda wannan magana. Sai Dawuda ya ce, “Zama surukin sarki ƙaramin abu ne a ganinku? Ga shi, ni talaka ne wanda ba sananne ba.”
24 Fādawan suka faɗa wa Saul abin da Dawuda ya faɗa.