39 Amma yaron bai san abin da ake nufi ba. Jonatan da Dawuda kaɗai suka san abin da ake ciki.
40 Sa'an nan Jonatan ya ba yaron makamansa, ya ce masa, “Kai su gari.”
41 Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsun, ya rusuna har sau uku. Sa'an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, amma Dawuda ya fi yi.
42 Jonatan ya ce wa Dawuda, “Sai ka tafi lafiya, tun da yake mun riga mun rantse wa juna da sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji zai zama shaida tsakanina da kai, da tsakanin zuriyarmu har abada.’ ” Dawuda ya yi tafiyarsa, Jonatan kuwa ya koma gari.