1 Sarki Dawuda ya tsufa ƙwarai, don haka ko an rufe shi da abin rufa ba ya jin ɗumi.
2 Saboda haka fādawansa suka ce masa, “Ranka ya daɗe bari mu nemo maka budurwa, wadda za ta zauna tare da kai, ta riƙa yin maka hidima, ta kwanta a ƙirjinka don ka riƙa jin ɗumi.”
3 Suka kuwa nemi kyakkyawar yarinya a dukan ƙasar Isra'ila. Sai suka sami Abishag a Shunem, suka kawo ta wurin sarki.
4 Ko da yake yarinyar kyakkyawa ce ƙwarai, ta zama mai lura da sarki, ta kuwa yi masa hidima, amma sarki bai yi jima'i da ita ba.
5 Adonija, dan da Haggit ta haifa wa Dawuda, ya ɗaukaka kansa cewa, “Zan zama sarki.” Ya kuwa shirya wa kansa karusai, da dakarai, da zagage hamsin a gabansa.
6 Tsohonsa bai taɓa tsawata masa ba. Shi kuma mutum ne kyakkyawa, an haife shi bayan Absalom.