37 Zan sa ka yi mulki a kan duk abin da ranka yake bukata, za ka zama Sarkin Isra'ila.
38 Idan za ka kasa kunne ga duk abin da na umarce ka, ka bi tafarkuna, ka aikata abin da yake daidai a gare ni, ka kiyaye dokokina da umarnaina kamar yadda bawana Dawuda ya yi, zan kasance tare da kai, zan sa gidanka ya kahu kamar yadda na sa gidan Dawuda ya kahu, zan ba ka Isra'ila.
39 Zan wahalar da zuriyar Dawuda, amma ba har abada ba.’ ”
40 Sulemanu kuwa ya nema ya kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tashi, ya tsere zuwa Masar, wurin Shishak Sarkin Masar, ya zauna a can har rasuwar Sulemanu.
41 Sauran ayyukan Sulemanu, da dukan abin da ya yi, da hikimarsa an rubuta su a littafin tarihin Sulemanu.
42 Sulemanu ya yi shekara arba'in yana sarauta a Urushalima a kan Isra'ila duka.
43 Sulemanu ya rasu, aka binne shi a birnin Dawuda, wato Urushalima. ‘Dansa Rehobowam ya gaji sarautarsa.