1 Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan mutanen Isra'ila sun tafi Shekem don su naɗa shi sarki.
2 Sa'ad da Yerobowam, ɗan Nebat, ya ji labari, gama a lokacin yana Masar inda ya gudu saboda sarki Sulemanu, sai ya komo daga Masar.
3 Suka aika a kirawo shi, sai Yerobowam da dukan taron jama'ar Isra'ila suka zo suka ce wa Rehobowam,
4 “Tsohonka ya nawaita mana, yanzu sai ka rage mana wahalar aikin tsohonka da nawayarsa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
5 Sai ya ce musu, “Ku tafi, ku sāke zuwa bayan kwana uku.” Sai suka tafi.