25 Sa'an nan sarki Yerobowam ya gina Shekem a ƙasar tudu ta Ifraimu, ya zauna can. Daga can kuma ya tafi ya gina Feniyel.
26 Yerobowam kuwa ya ce a zuciyarsa, “Mulkin fa zai koma gidan Dawuda.
27 Idan mutanen nan sun ci gaba da zuwa Urushalima don miƙa wa Ubangiji hadayu, zuciyarsu za ta koma kan sarki Rehobowam, na Yahuza, za su kashe ni, su koma wurinsa.”
28 Sai sarki Yerobowam ya yi shawara, ya siffata 'yan maruƙa biyu da zinariya. Sa'an nan ya ce wa jama'arsa, “Zuwanku Urushalima ya isa, yanzu ga allolinku, ya Isra'ilawa, waɗanda suka fito da ku daga ƙasar Masar.”
29 Ya kafa siffar maraƙi ɗaya a Betel, ɗayan kuma a Dan.
30 Wannan abu ya zama zunubi, gama mutane sun tafi wurin siffofin maruƙan nan a Betel da Dan.
31 Ya kuma gina masujadai a tuddai, sa'an nan ya sa waɗansu daga cikin mutane waɗanda ba Lawiyawa ba, su zama firistoci.