31 Bayan da ya binne shi, sai ya ce wa 'ya'yansa, “Sa'ad da na rasu, sai ku binne ni a kabarin da aka binne annabin nan. Ku ajiye gawata kusa da tasa.
32 Gama maganar Ubangiji da ya faɗa game da bagaden da yake cikin Betel, da masujadai na kan tuddai waɗanda suke a garuruwan Samariya, za ta cika.”
33 Bayan wannan al'amari Yerobowam bai bar muguwar hanyarsa ba, amma ya naɗa firistoci daga cikin mutane don masujadai da suke kan tuddai. Duk mutumin da yake so, sai ya keɓe shi don ya zama firist na masujada da take kan tudu.
34 Wannan zunubi ya zama sanadi ga gidan Yerobowam, har ya isa a shafe gidan, a hallaka shi ƙaƙaf.