1 Sar 14:21 HAU

21 Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi mulki a Yahuza. Yana da shekara arba'in da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi shekara goma sha bakwai yana sarauta a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka, domin ya sa sunansa ya kasance a wurin. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce.

Karanta cikakken babi 1 Sar 14

gani 1 Sar 14:21 a cikin mahallin