3 Shi kuma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa sosai, kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi ba.
4 Amma duk da haka, saboda Dawuda, Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima da ya sa ɗansa ya gāje shi, ya kuma kafa Urushalima,
5 domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.
6 Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa.
7 Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
8 Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.
9 A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowam Sarkin Isra'ila, Asa ya sarauci jama'ar Yahuza.