30 Wannan abu ya faru saboda zunubin Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi, ya tsokani fushin Ubangiji Allah na Isra'ila.
31 Sauran ayyukan Nadab, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
32 Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba'asha Sarkin Isra'ila dukan kwanakin sarautarsu.
33 A cikin shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ba'asha ɗan Ahija ya yi sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi shekara ashirin da huɗu yana sarauta.
34 Ya aikata zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi hanyar Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi.