31 Sauran ayyukan Nadab, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
32 Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba'asha Sarkin Isra'ila dukan kwanakin sarautarsu.
33 A cikin shekara ta uku ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ba'asha ɗan Ahija ya yi sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi shekara ashirin da huɗu yana sarauta.
34 Ya aikata zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi hanyar Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi.