1 Ubangiji ya yi magana da Yehu, ɗan Hanani a kan Ba'asha, ya ce,
2 “Tun da yake na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaban jama'ata Isra'ila, kai kuwa ka bi hanyar Yerobowam, ka sa jama'ata, wato Isra'ila, su yi zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu,
3 to, zan shafe ka da gidansa, in mai da gidanka kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat.
4 Duk mutumin da yake naka da zai mutu a cikin birni, karnuka ne za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura, tsuntsaye ne za su cinye shi.”