4 Duk mutumin da yake naka da zai mutu a cikin birni, karnuka ne za su cinye shi. Wanda kuma ya mutu a saura, tsuntsaye ne za su cinye shi.”
5 Sauran ayyukan Ba'asha, da dukan abin da ya yi, da irin ƙarfinsa, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
6 Ba'asha kuwa ya rasu, aka binne shi a Tirza. Sai Ila, ɗansa ya gāji sarautarsa.
7 Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba'asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.
8 A shekara ta ashirin da shida ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ila ɗan Ba'asha, ya ci sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi sarauta shekara biyu.
9 Amma Zimri, shugaban rabin karusan Ila, ya yi masa maƙarƙashiya. Sa'ad da Ila yake Tirza, ya sha, ya bugu a gidan Arza wanda yake lura da fāda,
10 sai Zimri ya shiga gidan, ya buge shi ya kashe shi. Wannan ya faru a shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza.