3 Sai Iliya ya ji tsoro, ya tashi, ya tsere zuwa Biyer-sheba ta Yahuza.Ya bar baransa a can.
4 Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”
5 Iliya kuwa ya kwanta, ya yi ta barci a gindin itacen. Farat sai mala'ika ya taba shi, ya ce masa, “Tashi, ka ci abinci.”
6 Da ya duba, sai ga waina da zafinta a bisa duwatsu, da butar ruwa a waje ɗaya. Ya ci, ya sha, ya koma kwantawa.
7 Mala'ikan Ubangiji kuma ya sake zuwa sau na biyu, ya taɓa shi, ya ce, “Tashi, ka ci abinci, in ba haka ba kuwa tafiya za ta gagare ka.”
8 Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.
9 A can ya shiga wani kogo domin ya kwana.Ba labari sai Ubangiji ya yi magana da shi, ya ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”