1 Ben-hadad Sarkin Suriya kuwa ya tara dukan sojojinsa. Sarakuna talatin da biyu kuma suna tare da shi, da dawakai, da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya yaƙi. Ya kuwa yi yaƙi da ita.
2 Sai ya aika da jakadu zuwa cikin birni wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce masa, “In ji Ben-hadad,
3 ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne, matanka kuma mafi kyau da 'ya'yanka nawa ne!’ ”
4 Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya amsa, ya ce, “Ya maigirma sarki, kamar yadda ka faɗa, ni naka ne da dukan abin da nake da shi.”