15 Sai ya tara sojoji matasa na hakiman larduna, mutum ɗari biyu da talatin da biyu. Sa'an nan kuma, ya tara dukan mutanen Isra'ila dubu bakwai (7,000).
16 Suka tafi da tsakar rana sa'ad da Ben-hadad yake a buge da sha a sansani, shi da sarakuna talatin da biyu waɗanda suka taimake shi.
17 Samarin ne suka fara fita. Sai Ben-hadad ya aiki mutane, suka faɗa masa cewa, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”
18 Sai ya ce, “Ku kama su da rai, ko sun zo da nufin salama ko da na yaƙi.”
19 Waɗannan kuwa suka fita daga birnin, wato sojoji matasa, rundunar Isra'ilawa kuma tana biye da su,
20 kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra'ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.
21 Sarkin Isra'ila ya fita, ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Suriyawa da yawa.