1 Sar 20:27-33 HAU

27 Aka tara mutanen Isra'ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra'ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar 'yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.

28 Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama'a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.’ ”

29 Suka kafa sansani daura da juna kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin, suka kama yaƙi. Isra'ilawa suka kashe Suriyawa mutum dubu ɗari (100,000) a rana ɗaya.

30 Sauran kuwa suka gudu zuwa birnin Afek. Garun birnin kuma ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai (27,000) waɗanda suka ragu.Ben-hadad kuwa ya gudu ya shiga ƙurewar ɗaki, a cikin birnin.

31 Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra'ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa'an nan mu tafi wurin Sarkin Isra'ila, watakila zai bar ka da rai.”

32 Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra'ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.”Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan'uwana ne.”

33 Da ma abin da fādawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan'uwanka, Ben-hadad.”Sarki Ahab ya ce musu, “Ku je ku kawo shi.” Ben-hadad kuwa ya zo wurinsa. Ahab ya sa ya shiga tare da shi cikin karusarsa.