33 Da shugabannin karusan yaƙi suke gane ba Ahab ba ne, sai suka rabu da shi.
34 Wani sojan Suriya kuwa ya yi sa'a, ya shilla kibiya kawai, sai ta sami Ahab, ta kafar sulkensa. Saboda haka ya ce wa mai korar karusarsa, “Ka juya, ka fitar da ni daga fagen fama gama an yi mini rauni.”
35 A ran nan yaƙi ya yi tsanani. Aka tallafi Ahab a cikin karusarsa a gaban Suriyawa. Da maraice ya mutu. Jinin raunin da aka yi masa ya zuba a cikin karusar.
36 A wajen faɗuwar rana aka yi wa sojoji shela aka ce, “Kowa ya koma garinsu da ƙasarsu.”
37 Sarki Ahab ya mutu, aka kawo shi Samariya, aka binne shi.
38 Suka wanke karusarsa a tafkin Samariya. Karnuka suka lashe jininsa, karuwai kuma suka yi wanka a tafkin kamar yadda Ubangiji ya faɗa.
39 Sauran ayyukan Ahab da dukan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.