41 “Sa'ad da kuma baƙo wanda yake wata ƙasa mai nisa ya ji labarin sunanka,
42 da manyan al'amura da ka yi wa jama'arka, ya zo domin ya yi maka sujada, da kuma addu'a gare ka a wannan Haikali,
43 sai ka kasa kunne ga addu'arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama'arka, Isra'ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.
44 “Idan jama'arka sun tafi su yi yaƙi da abokan gābansu, idan sun yi addu'a a gare ka, suna fuskantar birnin nan da ka zaɓa, da Haikalin nan wanda na gina saboda sunanka,
45 sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Ka ji daga sama, ka ba su nasara.
46 “Idan jama'arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,
47 idan sun koma cikin hankalinsu a ƙasar da aka kai su bauta, har suka tuba, suka roƙe ka a ƙasar, suna hurta zunubansu da irin muguntar da suka aikata, ka ji addu'arsu, ya Ubangiji.