44 “Idan jama'arka sun tafi su yi yaƙi da abokan gābansu, idan sun yi addu'a a gare ka, suna fuskantar birnin nan da ka zaɓa, da Haikalin nan wanda na gina saboda sunanka,
45 sai ka kasa kunne ga addu'arsu. Ka ji daga sama, ka ba su nasara.
46 “Idan jama'arka sun yi maka zunubi, gama ba mutumin da ba ya yin zunubi, har ka yi fushi da su, ka kuwa bashe su a hannun abokan gāba, har suka kwashe su zuwa bauta a wata ƙasa mai nisa,
47 idan sun koma cikin hankalinsu a ƙasar da aka kai su bauta, har suka tuba, suka roƙe ka a ƙasar, suna hurta zunubansu da irin muguntar da suka aikata, ka ji addu'arsu, ya Ubangiji.
48 Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,
49 sai ka ji addu'arsu da roƙe-roƙensu daga Sama, wurin zamanka, ka amsa, ka ji ƙansu.
50 Ka gafarta dukan zunubansu, da tayarwar da suka yi maka. Ka sa abokan gabansu su ji tausayinsu.