15 Wannan shi ne lissafin aikin tilas da sarki Sulemanu ya sa domin ginin Haikalin, da na fādarsa, da kuma Millo, a kuma gina garun birnin. Ya kuma sa tilas a sāke gina garuruwan Hazor, da Magiddo, da Gezer.
16 Gama Fir'auna ya haura, ya ci Gezer, ya ƙone ta da wuta, ya kuma kashe masu zama cikinta. Sa'an nan ya yi wa 'yarsa, wato matar Sulemanu, kyauta da Gezer ɗin.
17 Sulemanu kuwa ya sāke gina Gezer. Ya kuma sa aka gina Bet-horon ta kwari ta aikin tilas,
18 da Ba'alat, da Tadmor a cikin jeji, a ƙasar Yahuza,
19 da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.
20-21 Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, da suka ragu a ƙasar, wato waɗanda ba mutanen Isra'ila ba, waɗanda mutanen Isra'ila ba su iya hallakarwa ba, Sulemanu ya sa zuriyarsu su yi aikin tilas na bauta, haka kuwa suke har wa yau.
22 Sulemanu bai mai da mutanen Isra'ila bayi ba, amma su ne sojojinsa da dogaransa, da shugabannin sojoji, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.