18 da Ba'alat, da Tadmor a cikin jeji, a ƙasar Yahuza,
19 da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.
20-21 Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa, da suka ragu a ƙasar, wato waɗanda ba mutanen Isra'ila ba, waɗanda mutanen Isra'ila ba su iya hallakarwa ba, Sulemanu ya sa zuriyarsu su yi aikin tilas na bauta, haka kuwa suke har wa yau.
22 Sulemanu bai mai da mutanen Isra'ila bayi ba, amma su ne sojojinsa da dogaransa, da shugabannin sojoji, da shugabannin karusansa, da mahayan dawakansa.
23 Sulemanu yana da masu lura da aiki su ɗari biyar da hamsin, suna lura da masu aikin tilas a wurare dabam dabam da ake wa Sulemanu gini.
24 Da 'yar Fir'auna matar Sulemanu ta fita birnin Dawuda, zuwa gidan kanta wanda Sulemanu ya gina mata, sa'an nan ya gina birnin Millo.
25 Sau uku a shekara Sulemanu yakan miƙa hadayu na ƙonawa, da na salama, da hadayar turare, a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji. Ta haka aka gama ginin Haikali.