11 Wannan shi ne labarin manyan jarumawan Dawuda. Yashobeyam ɗan Bahakmone shi ne shugaban jarumawa talatin. Ya karkashe mutum ɗari uku da māshinsa baki ɗaya.
12 Na biye da shi shi ne Ele'azara ɗan Dodo, Ba'ahohiye, wanda yake ɗaya daga cikin manyan jarumawan nan uku.
13 Yana tare da Dawuda a Efes-dammin sa'ad da Filistiyawa suka taru wuri ɗaya don su yi yaƙi. Akwai wata gonar sha'ir a wurin, sai jama'a suka gudu daga gaban Filistiyawa.
14 Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha'ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya cece su, ya ba su babbar nasara.
15 Wata rana sai uku daga cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara zuwa dutsen Dawuda, a kogon Adullam, sa'ad da rundunar sojojin Filistiyawa suka kafa sansani a kwarin Refayawa.
16 Dawuda yana cikin kagara, sojojin Filistiyawa kuwa suna a Baitalami.
17 Sai Dawuda ya yi marmarin gida, ya ce, “Dā ma wani ya kawo mini ruwa daga rijiyar da take a ƙofar Baitalami in sha!”