13 Yana tare da Dawuda a Efes-dammin sa'ad da Filistiyawa suka taru wuri ɗaya don su yi yaƙi. Akwai wata gonar sha'ir a wurin, sai jama'a suka gudu daga gaban Filistiyawa.
14 Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha'ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya cece su, ya ba su babbar nasara.
15 Wata rana sai uku daga cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara zuwa dutsen Dawuda, a kogon Adullam, sa'ad da rundunar sojojin Filistiyawa suka kafa sansani a kwarin Refayawa.
16 Dawuda yana cikin kagara, sojojin Filistiyawa kuwa suna a Baitalami.
17 Sai Dawuda ya yi marmarin gida, ya ce, “Dā ma wani ya kawo mini ruwa daga rijiyar da take a ƙofar Baitalami in sha!”
18 Sai uku ɗin suka kutsa kai, suka shiga sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take a ƙofar Baitalami, suka ɗauka, suka kawo wa Dawuda, Dawuda kuwa bai sha ba, amma ya kwarara ruwan a ƙasa domin sadaka ga Ubangiji.
19 Sa'an nan ya ce, “Allah ya sawwaƙe mini da zan yi wannan abu a gabansa, da zan sha jinin waɗannan da suka sadaukar da rayukansu, gama sai da suka yi kasai da ransu, sa'an nan suka ɗebo ruwan.” Saboda haka bai sha ruwan ba. Manyan jarumawan nan uku ne suka aikata waɗannan abubuwa.