8 Sai Dawuda da dukan Isra'ilawa suka yi rawa da iyakar ƙarfinsu a gaban Allah, suna raira waƙoƙi suna kaɗa, garayu, da molaye, da ganguna, da kuge, suna busa ƙaho.
9 Sa'ad da suka kai masussukar Kidon, sai Uzza ya miƙa hannunsa don ya riƙe akwatin alkawarin saboda gargada.
10 Sai Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take a gaban Allah, saboda ya miƙa hannunsa ya kama akwatin alkawari.
11 Sai Dawuda ya ɓata ransa saboda da Ubangiji ya hukunta Uzza da fushi, sai ya sa wa wannan wuri suna Feresa-uzza, wato hukuncin Uzza.
12 Sa'an nan Dawuda ya ji tsoron Allah, ya ce, “Ƙaƙa zan kawo akwatin alkawarin Allah a gidana?”
13 Don haka Dawuda bai kai akwatin alkawarin zuwa cikin birninsa ba, amma ya raɓa da shi zuwa gidan Obed-edom wanda yake daga Gat.
14 Akwatin alkawarin Allah kuwa ya kasance a gidan Obed-edom har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa iyalin Obed-edom da dukan abin da yake da shi albarka.