5 Sa'ad da Suriyawa daga Dimashƙu suka zo don su taimaki Hadadezer Sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe mutum dubu ashirin da dubu biyu (22,000) daga cikin Suriyawan.
6 Sa'an nan Dawuda ya sa ƙungiyoyin sojoji a Suriya ta Dimashƙu, Suriyawa kuma suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.
7 Dawuda kuma ya ƙwato garkuwoyi na zinariya waɗanda barorin Hadadezer suke ɗauke da su, ya kawo su Urushalima.
8 Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali.
9 Sa'ad da Toyi, Sarkin Hamat, ya ji an ce Dawuda ya riga ya ci nasara a kan sojojin Hadadezer, Sarkin Zoba,
10 sai ya aiki Adoniram ɗansa wurin sarki Dawuda, don ya gaishe shi, ya kuma yabe shi saboda ya yi yaƙi da Hadadezer, har ya ci shi, gama Hadadezer yakan yi yaƙi da Toyi. Adoniram kuwa ya kawo kayayyaki iri iri na zinariya, da na azurfa, da na tagulla.
11 Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan ga Ubangiji, tare da azurfa da zinariya waɗanda ya kwaso daga al'umman da ya ci, wato Edom, da Mowab, da mutanen Ammon, da na Filistiya, da na Amalek.