4 Surukarsa Tamar, matar ɗansa kuma ta haifa masa Feresa da Zera. Yahuza yana da 'ya'ya maza biyar.
5 'Ya'yan Feresa, maza kuwa, su ne Hesruna da Hamul.
6 'Ya'yan Zera, maza, su ne Zabdi da Etan, da Heman, da Kalkol, da Darda. Su biyar ke nan.
7 Karmi shi ne mahaifin Akan wanda ya jawo wa Isra'ila wahala a kan abin da aka haramta.
8 Etan yana da ɗa guda ɗaya, shi ne Azariya.
9 'Ya'yan Hesruna, maza, waɗanda aka haifa masa, su ne Yerameyel, da Arama, da kuma Kalibu.
10 Arama shi ne mahaifin Amminadab. Amminadab kuma shi ne mahaifin Nashon, shugaban 'ya'yan Yahuza.