1 Sa'an nan sai Dawuda ya ce, “A nan Haikalin Ubangiji Allah zai kasance, da kuma bagaden ƙona hadaya domin Isra'ila.”
2 Dawuda kuwa ya umarta a tattaro dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila. Ya sa waɗansu su farfasa duwatsu, su sassaƙe duwatsun domin ginin Haikalin Allah.
3 Dawuda kuma ya cika manyan ɗakunan ajiya da ƙarafa don yin ƙusoshi na ƙyamaren ƙofofi, da mahaɗai, ya kuma tara tagulla mai yawa wanda ta fi ƙarfin awo,
4 da katakan al'ul da ba a san adadinsu ba, gama Sidoniyawa da mutanen Taya sun kawo wa Dawuda itacen al'ul mai ɗumbun yawa.