21 'Ya'yan Merari, su ne Mali da Mushi. 'Ya'yan Mali su ne Ele'azara da Kish.
22 Ele'azara kuwa ya rasu ba shi da 'ya'ya maza, sai 'yan mata kaɗai, sai 'yan'uwansu, 'ya'yan Kish, maza, suka aure su.
23 'Ya'yan Mushi, maza, su uku ne, wato Mali, da Eder, da Yerimot.
24 Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga gidajen kakanninsu, wato su ne shugabannin da aka rubuta sunayensu ɗaya ɗaya daga mai shekara ashirin da haihuwa zuwa sama. Su ne za su yi hidima a cikin Haikalin Ubangiji.
25 Gama Dawuda ya ce, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya hutar da jama'arsa, yana kuwa zama a Urushalima har abada.
26 Yanzu Lawiyawa ba za su riƙa ɗaukar alfarwar sujada tare da kayayyakin yin aiki a cikinta ba.”
27 Bisa ga maganar Dawuda ta ƙarshe aka ƙidaya 'ya'yan Lawiyawa, maza, daga mai shekara ashirin zuwa sama.