27 Na wajen Merari, wato na wajen Yayaziya, su ne Beno, da Shoham, da Zakkur, da Ibri.
28 Na wajen Mali, shi ne Ele'azara wanda ba shi da 'ya'ya maza.
29 Na wajen Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel.
30 'Ya'yan Mushi, maza, su ne Mali, da Eder, da Yerimot.Waɗannan su ne 'ya'yan Lawiyawa, maza, bisa ga gidajen kakanninsu.
31 Su ma suka jefa kuri'a kamar yadda 'yan'uwansu, 'ya'yan Haruna, maza, suka yi a gaban sarki Dawuda, da Zadok, da Ahimelek, da shugabannin gidajen kakanni na firistoci da na Lawiyawa. Shugaban gidan kakanni ya jefa kuri'a daidai da ƙanensa.