1 Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na 'ya'yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.
2 Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,
3 amma Allah bai yardar mini in yi da kaina ba, domin ni mayaƙi ne, na kuwa zubar da jini.
4 Duk da haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra'ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin 'ya'yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra'ila.
5 Daga cikin dukan 'ya'yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni 'ya'ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra'ila, abin mulkin Ubangiji.
6 “Ya ce mini, ‘Ɗanka Sulemanu ne zai gina Haikalina da shirayuna, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa in zama uba a gare shi.
7 Zan tabbatar da mulkinsa har abada idan ya bi umarnaina da ka'idodina da himma kamar yadda ake yi a yau.’