1 Ra'ubainu shi ne ɗan farin Isra'ila, amma saboda ya ƙazantar da gadon mahaifinsa aka ba 'ya'yan Yusufu, maza, ɗan Isra'ila, gādonsa na ɗan fari. Don haka ba a lasafta shi a kan matsayin ɗan fari ba.
2 Ko da yake Yahuza ya rinjayi 'yan'uwansa, har daga gare shi aka sami shugaba, duk da haka matsayin ɗan farin na Yusufu ne.
3 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, wato ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi.
4 'Ya'yan Yowel, maza, su ne Shemaiya, da Gog, da Shimai,