15 Ahi ɗan Abdiyel, wato jīkan Guni, shi ne shugaban gidan kakanninsu.
16 Suka zauna a Gileyad, da Bashan, da garuruwanta, da dukan iyakar makiyayar Sharon.
17 (An rubuta waɗannan duka bisa ga asalinsu a zamanin Yotam, Sarkin Yahuza, da Yerobowam Sarkin Isra'ila.)
18 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa suna da jarumawa masu riƙon garkuwa da takobi, masu harbi kuma da baka. Gwanayen yaƙi ne, su dubu arba'in da huɗu, da ɗari bakwai da sittin ne (44,760).
19 Suka yi yaƙi da Hagarawa, da Yetur, da Nafish, da Nodab.
20 Aka taimake su yin yaƙi da abokan gābansu, sai aka ba da Hagarawa da duk waɗanda suke tare da su a hannunsu, saboda suka yi roƙo ga Allah a cikin yaƙin, Allah kuwa ya amsa musu roƙonsu saboda sun dogara gare shi.
21 Sai suka kwashe dabbobinsu, raƙuma dubu hamsin (50,000), da tumaki dubu ɗari biyu da dubu hamsin (250,000), da jakuna dubu biyu (2,000), da kuma mutane dubu ɗari (100,000).