59 da Ayin tare da makiyayarta, da Bet-shemesh tare da makiyayarta.
60 Daga kabilar Biliyaminu aka ba su Geba tare da makiyayarta, da Allemet tare da makiyayarta, da Anatot tare da makiyayarta. Dukan biranen iyalansu guda goma sha uku ne.
61 Aka ba sauran 'ya'yan Kohat, maza, garuruwa goma daga na rabin kabilar Manassa, ta hanyar kuri'a.
62 Aka kuma ba Gershonawa bisa ga iyalansu, birane goma sha uku daga na kabilar Issaka, da na kabilar Ashiru, da na kabilar Naftali, da na kabilar Manassa da take nan a Bashan.
63 Haka kuma aka ba 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga na kabilar Ra'ubainu, da na kabilar Gad, da na kabilar Zabaluna.
64 Haka fa, jama'ar Isra'ila suka ba Lawiyawa garuruwa duk da makiyayansu.
65 Daga na kabilar Yahuza, da na kabilar Saminu, da na kabilar Biliyaminu kuma aka ba da waɗannan garuruwan da aka ambaci sunayensu ta hanyar kuri'a.