1 'Ya'yan Issaka, maza, su huɗu ne, wato Tola, da Fuwa, da Yashub, da Shimron.
2 'Ya'yan Tola, maza, su ne Uzzi, da Refaya, da Yeriyel, da Yamai, da Ibsam, da Sama'ila, su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Tola kuwa manyan mayaƙa ne a zamaninsu. Yawansu a zamanin Dawuda, su dubu ashirin da biyu ne da ɗari shida (22,600).
3 Ɗan Uzzi, shi ne Izrahiya. 'Ya'yan Izrahiya, maza, su ne Maikel, da Obadiya, da Yowel, da Isshiya. Su biyar duka manyan mutane ne.
4 A zamaninsu, bisa ga gidajen kakanninsu suna da sojoji dubu talatin da dubu shida (36,000) gama suna da mata da yara da yawa.
5 Mayaƙan da aka lasafta bisa ga asalinsu na dukan iyalan Issaka, su dubu tamanin da dubu bakwai ne (87,000), jarumawa ne sosai.